Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mutane Biliyan Guda Masu Amfani Da Dandalin Yahoo Aka Yiwa Kutse A Shekarar 2013


Kutsen bayanai da aka yi cikin watan Agustan shekarar 2013, ya kwarmata bayanan mutane sama da Biliyan guda masu amfani da dandalin yahoo a cewar kamfanin a jiya Laraba.

Kutsen da aka yi wa mutanen ya sha bam-bam da rahotan da kamfanin Yahoo ya fitar a cikin watan Satumba, inda kamfanin ya ce an saci bayanan mutane Miliyan 500, masu amfani da Yahoo a shekarar 2015.

Bayanan da aka sata sun hada da sunayen mutane da adireshin email dinsu da lambobin wayoyi, da kuma ranakun haihuwa da tambayoyin tsaro da amsoshinsu. Sai dai ana kyautata zaton wannan abu bai shafi takardun kudi da na bankuna ba, inji kamfanin.

Kamfanin Yahoo dake zaune a garin Sunnyvale, Jahar California, yana cikin shirye shiryen hadewa da kamfanin Verizon akan dalar Amurka Biliyan 4.8. Kamafanin dai bai bayyana na uku da ake zargi a kutsen na shekara ta 2013 ba.

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

XS
SM
MD
LG