Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mataimakin Gwamnan Borno Ya Rasu


FILE
FILE

Gwamnatin Jihar Borno dake arewa maso gabashin Najeriya ta tabbatar da rasuwar mataimakin gwamnan Jihar Borno Alhaji Zanna Umar Mustapha.

Marigayin ya rasu a birnin Yola dake Jihar Adamawa, a lokacin da yake ziyarar aikina bikin yaye dalibai da aka yi Asabar dinnan.

Bayan kwanciya da dare a makwancinsa, wayewar gari ke da wuya aka bincika aka ga ya rasu.

An yi korin neman Alhaji Zanna ta waya, bai dauki waya ba, kuma babu alamunsa ko motsin sa. Bayanan da muka samu sun bayyana mana cewa an karya kofar dakin da yake ciki, a nan ne aka same shi babu rai.

Ya zuwa yanzu babu bayanai dangane da ko yana fama da wata rashin lafiya. Saboda ko shekaran jiya a birnin Maiduguri, an yi zagayen aiki da shi a wasu kauyuka tare da gwamnan Jihar.

Marigayin yayi ayyuka da dama kafin ya tafi garin Yola. Bayanai da Sashen Hausa na Muryar Amurka ya samu na cewa babu wani rashin lafiya da yake tattare da shi, wanda ake zaton shi ne yayi sanadiyar rasuwar sa.

please wait

No media source currently available

0:00 0:07:12 0:00
Shiga Kai Tsaye

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Nijar Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:47 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Hira Ta Musamman Kan Nasarar Donald Trump Da Kayen Da Kamala Harris Ta Sha
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Shugabannin Kasashen Nahiyar Turai Suka Taya Donald Trump Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:55 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Zaben 2023

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Ghana Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:40 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Trump Da Magoya Bayanshi Suka Yi Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG