Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Zanga-Zanga: Egbetokun Ya Bada Umarnin Bincikar Zargin Kungiyar Amnesty Na Hannun ‘Yan Sanda A Mace-Mace


Zanga-zangar tsadar rayuwa a Najeriya
Zanga-zangar tsadar rayuwa a Najeriya

A jawabin Amnesty ta bayyana cewar wadanda aka kashe din sun hada da matasa 20, da dattijo guda da kuma kananan yara 2.

Babban sufeton ‘yan sandan Najeriya, Kayode Egbetokun ya bada umarnin gudanar da bincike a kan zargin rundunar ‘yan sandan kasar da hannu a kashe-kashe da kamen masu zanga-zangar neman kawo karshen tsadar rayuwa data gudana cikin watan Agustan daya gabata.

A jawabin data wallafa kwanakin da suka gabata, kungiyar kare hakkin dan adam ta Amnesty, ta zargi rundunar ‘yan sandan Najeriya da yin amfani da karfi fiye da kima akan masu zanga-zanga yayin boren neman kawo karshen tsadar rayuwar daya gudana tsakanin ranaikun 1 zuwa 10 ga watan Agustan daya gabata, inda aka hallaka akalla mutane 24 a jihohin Borno da Kaduna da Kano da Katsina da Jigawa da kuma Neja.”

A jawabin Amnesty ta bayyana cewar wadanda aka kashe din sun hada da matasa 20, da dattijo guda da kuma kananan yara 2.

A martanin da ya mayar a Abuja a yau Litinin cikin wata sanarwa, kakakin rundunar ‘yan sandan Najeriya, ACP Muyiwa Adejobi, yace akwai alamar “rashin gaskiya da rudani” a cikin zarge-zargen, inda ya kara da cewa Egbetokun ya bada umarnin gudanar da bincike a kan lamarin.

“Da kwakkwarar murya rundunarmu take musanta cewa wadannan zarge-zarge basu da tushe kuma babu kamshin gaskiya sannan sun ci karo da rahotannin yadda al’amura suka faru kamar yadda rundunonin dake jihohin da al’amari ya shafa suka aikewa ofishin babban sufeton ‘yan sandan Najeriya.”

“Rundunarmu na son jaddada cewa a tsawon lokacin zanga-zangar, ta gudanar da ayyukanta a bisa dacewa da dokokin kwantar da tarzoma, ciki har da samarda tsaro ga masu zanga-zangar lumana.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG