Sai dai duk da haka jama'a na kira ga gwamnati ta samar da wani shirin kayyade farashi domin talakawa su samu sa'ida a kasar.
Daukan wannan mataki dai in ji masana da 'yan kasa zai taimaka wajen karya farashin abinci da kuma wadata a kasa.
Alhaji Shehu Usman Sanfan shugaban 'yan kasuwan 12 a Legas ya shaida wa Muryar Amurka godiyarsu ga gwamnati ko da yake ya ce su ma a duba nasu kukan.
Ya ce kayan abinci irin na su an fara samun sauki domin ana shigo da shi daga makwabtan kasashe sakamkon bude boda, haka su ma masu hatsi da suka boye duk sun fara fito da shi.
Domin neman kazamar riba wasu ke sayan kayan su boye.
Ya ce don haka suna godewa gwamnati wannan mataki da ta dauka na shigo da abinci.
Tun bayan zanga-zangar da aka gudanar gwamnati ta ba da umarnin bude boda da cire haraji akan wasu kayan abinci, abunda ya taimaka wajen karya farashin abincin daga kasashen ketare.
Dr. Dauda Mohammed Kontagora ya ce dole ne gwamnati ta samar da tallafi na shigo da kayan masarufu da samar da wutan lantarki domin gina kananan masana'antun da samar da kayan gona da abinci domin dogaro da kai da kuma kauda talauci.
Yanzu dai a yayin da gwamnati ke alkawarin daukan matakan na karya farashin kayan masarufi, 'yan Najeriya sun zuru ido domin gani a kasa.
Saurari cikakken rahoto daga Babangida Jibrin:
Dandalin Mu Tattauna