Farashin kayan masarufin ya tashi ne da kashi goma sha takwas bisa dari ko fiye da haka abun da kasar ta dade da ganin irin hakan.
Tashin farashin, bayan kudin abinci, ya shafi gidaje da ruwan sha da wutar lantarki da man girki.
Abdullahi Umar wani dan kasuwa a Abuja ya bada tabbacin yadda lamarin yake a kasuwar Wuse dake cikin Abuja. Ya bada misali da madara mai kwaya dari da ada suke saye akan kudi nera dubu shida da dari biyar amma yanzu ya zama nera dubu shida da dari takwas kuma kwaya hamsin kacal gareshi maimakon dari, an samu karin farashin na dari da tara bisa dari ko 109%
Haka ma indomi da suke saye dubu daya da dari shida yanzu ana sayar dashi dubu uku da dari daya ko kuma karin 93%
Wani masanin tattalin arziki Yushau Aliyu yace hawa hawar farashi ba zai sauka ba kuma idan hakan ya cigaba rayuwar mutane zata shiga wata matsala saboda kudaden da mutane ke rike dasu ba zasu isa biya masu bukatunsu ba. Idan mutane basu iya sayen kaya ba ribar kamfanoni zata dinga raguwa har ta kaisu ga durkushewa.
Ga rahoton Saleh Shehu Ashaka da karin bayani.