A wani taron tattaunawa tare da hadin gwiwar jami’an ‘yan sandan Najeriya, kungiyar maus safarar kayayyakin gona da dabbobi ta bayyana cewa yawan kudin haraji da ake tsauwala ma ‘ya’yan kungiyar ne ke haifar da hauhawar fasashin kayan abinci da tsadar nama a fadain kasar.
Shugaban kungiyar na jihar Filato, Yusuf Samuel Haman, ya ce sun daura aniyar yaki da masu yi wa talakawa zagon kasa, ya kuma kara da cewa a duk lokacin da mai kaya ya lissafa kudaden da ya kashe domin biyan haraji kafin ya kai kayan inda zai sayar, wajibi ne ya kara farashi.
Ta dalilin haka ne ya yi kira ga daukacin jihohin Najeriya su cire wadannan mutane da ke neman hana manoma da makiyaya gudanar da harkokin kasuwanci yadda ya kamata.
Su ma shugabanin kungiyar Fulani ba a barsu a baya ba, domin kuwa sun bayyana irin akubar da suke fuskanta a kan hanyoyin kasar musamman yadda lamarin yake karewa kan makiyaya, domin a cewarsu, kasancewar masu amsar harajin bata hana wucewa da shanun sata.
Saurari rahoton Zainab Babaji domin karin bayani.
Facebook Forum