Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Daga Ilimin Kimiyya -Inji Next, Furodusa Kuma Injiniyan Waka Mai Hadawa Mawaka Sauti


Micheal Ekonoja Orji
Micheal Ekonoja Orji

Micheal Ekonoja Orji, wanda aka fi sani da Next – Ya ce a yanzu haka shi ne gwarzo a harkar sauti da waka wato AMMA award da ake ba mawaka, kuma burinsa a wannan shekara shine ya kara lashe wannan kyauta, kuma fatansa ya dauki lambar girman a kala sau biyu.

Next, ya ce ya fara harkar waka ne shekaru goma da suka wuce a matsayinsa na furudusa da kuma sound injiniya.

Matashin bayyana cewa yana hada wa mawakka sauti da taimaka wa wajen daukar muryoyinsu, wannan ya taimaka masa wajen sa masa ra’ayin son rera waka, wanda hakan yasa ya tsinci kansa cikin harkar waka mussamam ma wakar zaurance.

Michael ya ce yana hadawa masu finafinai sauti da kuma wasu sauran shirye shiryen gidajen rediyo, haka kuma da ya yi nisa a harkar ne ya fuskanci cewar sauti na daga cikin wani sashen da ilimin kimiyya da fasaha da ya koya a makaranta.

Matashin ya kara da cewa ya fara koyon ilimin kimiyya da fasaha a makaranta wanda hakan ya taimaka masa wajen hada sautuka, kuma kawo yanzu dai Next, yace ya reni akalla mutane biyar a harkar waka .

A fannin mu na tsegumi kuwa fitattaciyar mawakiyar nan Janet Jackson ta haihu a jiya, da santalelen jaririnta namiji tana mai shekaru 50 da haihu a duniya.

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:59 0:00

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

XS
SM
MD
LG