Jiya da dare dan takaran shugaban kasa na Amurka a karkashin lemar jam’iyyar Republicans, attajirin nan Donald Trump ya sha sukar lamiri kusan daga kowane bangare a lokacin muhawara ta biyu da aka gudanar a tsakanin abokan takaran nashi, wadanda da yawansu suka ce bai cancanta ya ja ragamar shugabancin Amurka ba.
Duka-duka jimillar ‘yantakara goma-sha-daya ne suka yi wannan muhawarar a cikin Gidan Tarihi na tsohon shugaban Amurka Ronald Reagan dake Simi Valley a jihar California.
A lokacin muhawarar, Donald Trump yayi ta jadadda kwarewarsa a harakar kasuwanci, yace kuma yana da fasahar cudanaya da jama’a kuma zai iya aiki da shugabannin kasashen duniya daban-daban ciki harda na Rasha, Vladimir Putin.
Magangannu masu gauni da suka hada da shirin da ya bayyana na koran ‘yan gudun hijira milyan 11 dake Amurka na daga cikin abinda ya karawa Trump tagomashi, har ya shige gaban sauran abokan takaran nashi, har gashi yanzu shi kadai ne yakeda tagomashi 27% na Amurkawa, yayinda wani tsohon likita Ben Carson, wanda Bakar Fata ne, ke da 23%.
Sauran wadanda ke neman jam’iyyar tasu ta Republicans ta basu tikitin tsaya mata zaben shugaban kasan da za’ayi badi sun hada da tsohon sgwamnan jihar Florida, Jebb Bush, da Danmajalisar Dattawa Rand Paul, gwamnan jihar New Jersey, Chris Christie da kuma mace daya tilau, Carly Fiorina.