Babbar alamar mulkin dimokiradiyar Amurka na kusan shekaru 250 shine yadda ake musayar ikon shugabancin kasar duk bayan shekaru 4, kuma hakan na daf da faruwa a yau Litinin, inda ake shirin sake rantsar da Donald Trump, Shugaban Amurka na 45 kafin yayi rashin nasara a takararsa ta 2020, a matsayin shugaban kasar na 47 biyo bayan nasarar daya samu a zaben daya gudana a watan Nuwamban daya gabata.
Ana sa ran milyoyin Amurkawa zasu kalli yadda Trump, mai shekaru 78, zai sake karbar rantsuwar kama aiki a sabon wa’adin mulki na shekaru 4 a fadar White House yayin da Joe Biden, mai shekaru 82, zai bar fadar bayan kammala wa’adin mulki daya, ta akwatunan talabijin dinsu.
Sai dai kimanin mutane 600 ne kadai zasu shaida rantsar da Trump din kai tsaye, sakamakon mayar da bikin babban dakin taro na Majalisar Dokokin Amurka da aka yi bisa umarnin Trump din.
Busawar iska mai sanyi a birnin Washington a daren jiya Lahadi na iya sauke yanayin sanyi da tsakar ranar yau litin zuwa mizanin -6 a ma’aunin Celsius, inda a bisa al’ada an saba gudanar da bikin rantsawar akan matakalar shiga Majalisar Dokokin kasar ta Capitol dake kallon farfajiyar dake tsakaninta da fadar White House.
Ana sa ran wannan bikin rantsarwar ya zama mafi tsananin sanyi da aka gani a birnin Washington cikin shekaru 40, sa’ilin da aka mayar da bikin rantsar da Ronald Reagan a hawansa na 2 cikin ginin majalisar a 1985.
An riga an rabawa magoya baya da manyan baki tikitin kallon bikin rantsar da Trump a sarari kan matakalar shiga Majalisar Dokokin Amurka ta Capitol guda 250, 000, saidai jami’an shirya bikin sun ce yanzu zasu iya adana tikitin a matsayin tsarabar tunawa da bikin.
Yanzu an soke faretin al’ada da aka saba yi akan titin Pennsylvania daga ginin Majalisar Capitol zuwa fadar White House saboda yanayi, saidai kungiyoyin makada da masu fareti da makamantansu zasu wuce ta gaban Trump da matarsa Melania da sauran jami’an sabuwar gwamnatinsa a cikin rufaffan dandalin “Capital One” mai daukar mutane 20, 000, inda za’a cewa an kyale dubban mahalarta bikin a waje cikin sanyi.
Trump zai kasance wanda ya aikata babban laifi na farko daya zama shugaban Amurka, bayan da wata kotu a bara ta same shi da laifi a tuhume-tuhume 34 dake da nasaba da shirya bayanan kasuwancin bogi domin boye toshiyar bakin dala 130, 000 daya biya wata jarumar fina-finan batsa stormy daniels, duk da cewar alkalin yaki amincewa ya hukunta shi ta kawone hali.
Dandalin Mu Tattauna