Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Trump Ya Shirya Wani Gangami Wuni 1 Gabanin Rantsar Da Shi


US President-elect Donald Trump arrives to speak at a MAGA victory rally at Capital One Arena in Washington, DC on January 19, 2025, one day ahead of his inauguration ceremony. (Photo by Jim WATSON / AFP)
US President-elect Donald Trump arrives to speak at a MAGA victory rally at Capital One Arena in Washington, DC on January 19, 2025, one day ahead of his inauguration ceremony. (Photo by Jim WATSON / AFP)

“Zamu Tabbata mun yi aikin da zai shafe koma bayan Da Amurka ta fuskanta na shekaru hudu (4) a ranar farko da muka kama aiki...

A jajiberin ranar ratsar da sabon shugaban kasa Donald Trump, magoya bayan shi sun gudanar da wani gangami jiya Lahadi a matsayin matakin farko na kafa sabon gwamnatin tarayya, wanda ya sauya abubuwan da suka fi mahimmanci ga gwamnatin tarayya ba tare da bata lokaci kana ya tabbatar da cewa “an rushe shafin wa’adin shekaru 4 na komabayan Amurka),”

Magoya bayan Trump sunyi dafifi a dandalin Capital One Arena a cikin birnin Washington DC domin hallartar bukin murnar “Make America Great Again” da wadanda suka yi ta Shewa da Trump y ace zai dau matakan gaggawa akan duk alkawuran da yayi, daga kamen bakin Hauren dake shigowa Amurka ta barauniyar hanya a kan iyakar Amurka da Mexico zuwa kara kaimi wa bagaren hakko danyen mai, da tsarin ma’aikatan gwamnatin tarayya da kawar da shirye shirye daban daban.

“Zamu Tabbata cewa munyi aikin da za a sheda ranar farko da muka kama aiki ya kasance ranar da ta fi ko wace, makon farko ya kasance mafi girma cikin kwanaki 100 na farko a tarihin shugabancin Amurka,” inji Trump, wanda ya kuma yi alkawarin jingine da shirye-shiryen shugaba Joe Biden mai barin gado cikin sa’o’i.

A wani yanayi ba saban ba, Trump ya shiga dandalin a wani bangaren da babu mutane sannan da gangan ya bi matakala ya sauka gabanin jawabin shi, inda yayi tsaya wa da hannunsa dukule sannan ya tsaya akayi masu hoto da mahallarta gangamin.

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG