Yace gwamnati yakamata ta sani cewa wannan ta'adancin ya fi karfin a yakeshi da karfin soja. Dole ne gwamnati ta nemi yadda zata zauna da 'yan tsageran ta daidaita da su. Dole a nemi masalaha amma idan an cigaba da yadda ake babu abun da za'a iya cimma sai dai a cigaba da asarar rayuka.
Shi ma Dr Bawa Abdullahi Wase masanin harkar tsaro a kasar ya bukaci shugabannin kasar su yi karatun ta natsu game da abubuwan dake faruwa inda yanzu kodayaushe kungiyar Boko Haram ta ga dama zata kai hari musamman a jihar Borno. Kwamitin Turaki da gwamnatin tarayya ta kafa ya bada shawara yadda za'a zauna da wadannan masu korafi a samu a daidaita da su. A duk fadin duniya haka ake yi. Yace Amurka ta yi haka. Kasar Rasha ma ta yi. Kai ba'a dade ba da Ingila ta daidaita da 'yan tsagerun Ireland ta Arewa. Lokacin 'yan neja Delta shugaban kasa mai ci ai ya zauna dasu ya sasanta da su ya basu kudi aka kuma koya masu ayyukan yi. Har yanzu ana cigaba da shirin da Shugaba Musa Yar'adua ya bari inda ake basu kaso mai tsoka daga kasafin kudin kasar.
Idan dan arewa lokacin da yake shugabanci ya nemi zaman lafiya da bangaren da ba nashi ba ta yaya za'a ce shugaban yanzu ya tura sojoji su je suna kashe mutane daga wani bangere da ba nashi ba maimakon ya yi abun da da aka yi, wato zaman sulhu da 'yan tsageran. Idan aka cigaba da hakan to babu inda za'a je , zaman lafiya kuma saidai ya zama tasuniya.
Wani da rikicin ya rutsa da shi yace lokaci yayi da gwamnonin arewa zasu fito su rungumi gaskiya dake cikin wannan dambarwar. Su fito gaskiya su fadawa shugaban kasa ya karo jami'an tsaro da kayan aiki idan kuma zaunawa za'a yi dasu to a hanzarta a yi hakan. Sa sojoji bakwai a karamar hukuma daya bashi da ma'ana. Don haka ya kamata a daina kame-kame.