'Yan gudun hijiran dake tsugune a garuruwan Gulak da Madagali jihar Adamawa sun hada da mata da yara wadanda suka zama abun tausayi. Wakilin Muryar Amurka da shi ma ya kai ziyara ya ga yara suna kuka mata kuma suna kwalla dukansu cikin halin lahaula wala kawati.
Yayin da gwamnan ya je garin Gulak shi ma yana magana yana kwalla ganin irin halin da mutanensa suka fada ciki musamman idan an yi la'akari da cewa wadannan mutane ne da basu ci ba basu sha ba.
A jawabin da gwamna Kashim Shettima ya yi masu ya basu hakuri. Ya fada masu cewa su ma sun damu da abun da yake faruwa a jihar. Ya ce da can gwamnati ta bada taimakon nera miliyan dari daya. Yanzu kuma ta kara nera miliyan dari daya. Sanata Ndume yana cikin tawagar da ta ziyarci 'yan gudun hijiran. Yace kowa ya san abun da ya kawo su domin haka suna ba mutane hakuri da bada tabbacin taimako daga kwamnati.
Gwamnan ya ziyarci sarkin garin wanda yace kawo yanzu duk mutane kauyukan sun gudu domin banda kashe-kashe gidajensu ma an konesu tare da gonakansu. Wuraren ibada ma basu tsira ba domin maharan sun kone masallatai da coci coci.
Ga Haruna Dauda Biu da cikakken rahoto.