Wannan dai na zuwa ne yayinda ake cigaba da jimamin kwanton baunan da wasu ‘yan bindiga suka yi wa sojoji a yankin Izge, yayin da sojojin ke kan hanyar kai ceto.
Da yake tabbatar da halin da al-umman kan iyakar ke ciki da kuma kwanton baunan da aka yi wa sojojin, daya daga cikin shuwagabannin karamar hukumar Madagali, Mr. Maina Uluramo yace ‘yan bindiga sun tarwatsa al-ummomi da dama, saboda haka ne suke kiran a kafa rundunana musamman a yankin.
Mr. Maina yace “an kawo zuwa Izge, to su kuma mutanen Izge suna guduwa zuwa Madagali. Muna kiran gwamnati ta dauki mataki akan wannan abun, a san yanda za’a yi tsare wannan waje inda mutane suke”.