Shaidu suka ce dakarun sun auna wani taro a unguwar da ake kira Balbala, wadanda suke addu'o'i na tunawa da wani shugaban addini marigayi Sheikh Yonis Muse.
Kamar yadda wasu majiyoyi suka yi bayani jami'an tsaron sun kai somame kan wurin taron da misalin karfe 5 na asubahi, suka bude wuta.
Wani wakilin Muryar Amurka a Djibouti yace wasu fiye da mutane 10 sun jikkata kari kan wadanda aka kashe.
Gwamnatin kasar tace, jami'an tsaron sun bude wuta ne bayan wasu mutane dauke da makamai suka kai musu hari.
A cikin sanarwar da ministan harkokin cikin gidan kasar Hassan Omar Mohammed ya bayar, ya aza laifin kan wata makarkashiya da makiyan kasar da ketare suka kitsa. Ya kara da cewa an kuma kama wasu mutane masu yawa dangane da lamarin.