Jami'ai sun bayyana cewar 'yan tsagerar sun kaiwa mutane masu yawa hare-haren ta'addanci, cikinsu harda jami'an 'yan sanda, an kuma kashe farar hula masu yawa. Su dai 'yan kungiyar al-Shabab sun yi ikrarin cewar sune ke kai irin wadannan hare-haren a kan farar hula, sun kuma kashe mutane masu yawa 'yan Somalia da 'yan kasar Djibouti.
Kasar Djibouti dai, na daya daga cikin kasashen dake bada agajin sojin dake tallafawa rundunar sojin kiyaye zaman lafiya ta kungiyar tarayyar Afirka dake Somalia. Idan an tuna, a watan da ya gabata ne kungiyar Al-shabab tayi ikrarin cewar ita keda alhakin kai harin bom a gidan cin abinchi Beletweyne inda har aka kashe akalla mutane 15.