Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Majalisar Adamawa na Zargin Ana Yiwa Rayuwarsu Barazana


Murtala Nyako, gwamnan Jihar Adamawa
Murtala Nyako, gwamnan Jihar Adamawa

Yayin da 'yan kwamitin mutane bakwai da mukaddashin alkalin alkalan jihar Adamawa ya kafa domin ya binciki gwamnan jihar da mataimakinsa bisa ga zargin da 'yan majalisa suke yi masa, yanzu 'yan majalisar sun ce ana yiwa rayuwarsu barazana.

Da soma zaman kwamitin binciken gwamnan jihar Adamawa da mataimakinsa, sai gashi 'yan majalisar jihar na zargin cewa ana yiwa rayuwarsu barazana.

Sakataren yada labaran majalisar Mr. Solomon Kumanga yace sun bankado wani yunkurin kai masu hari tare kuma da sace wasunsu. Amma yace yunkurin ba zai razanasu ba. Yace wai an kawo 'yan bindiga dadi su harbesu su ko kuma su sace wasu domin kada su iya cigaba da gudanar da binciken da aka soma yanzu. Kakakin yace sun samu hujjoji daga jami'an tsaro da wasu mutane.

A cewar kakakin wai ana rabar da hotunan 'yan majalisar domin su 'yan bindigar su ganesu su kuma hallakasu ba tare da yin kuskure ba tunda basu san 'yan majalisar ba. An dauki matakan tsaro. Kowane dan majalisa an tura masa jami'an tsaro domin kare lafiyarsu.

To saidai jam'iyyar APC ta bakin kakakinta Mr. Sabio ta mayar da martani inda tayi watsi da zargin 'yan majalisar. Kakakin yace duk lokacin da mutum ya taka doka dole ya ji tsoro. Ko inuwarka na iya baka tsoro domin ka san baka aikata daidai ba. Su 'yan majalisar sun sani cewa abun da suke yi ba domin jihar Adamawa su keyi ba. Duk abun da aka yi bisa zalunci dole a tsorata.

Ita ma rundunar 'yansandan jihar ta bakin kakakinta DSP Usman Abubakar tace bata da masaniya akan yunkurin amma ta dauki duk matakan kare rayuka da kuma dukiyoyin jama'a.

Ga rahoton Ibrahim Abdulaziz.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:00 0:00
Shiga Kai Tsaye

Alkaluma daga watan Janairu sun nuna ana ci gaba da samun hauhawar farashin kayan abinci, na mai da na gidaje da sauransu a Amurka
please wait
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p

No media source currently available

0:00 0:03:02 0:00
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Zaben 2023

Bayan wasu shekaru kasuwanni na rufe saboda matsalar tsaro a yankin Birnin Gwari na jihar Kaduna, a yanzu harkoki sun fara dawowa
please wait
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p

No media source currently available

0:00 0:02:31 0:00
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
Malam Bello Abba Yakasai masani kan harkokin noma ya yi karin haske akan matsalar tsaro ga manoma da hanyoyin magance wannan matsala
please wait
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 810p
  • 720p

No media source currently available

0:00 0:04:20 0:00
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 810p
  • 720p
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG