Kasa da makonni biyu da kawo karshen taron kasa da gwamnatin tarayya ta shirya daya daga cikin mahalarta taron daga arewa yace taron ya yiwa arewa alfanu.
Sanata Saidu Umar Kumo yace zuwa taron alheri ne ga arewa. Taron ya nuna karara irin hazukan mutane da kasar ke dasu musamman arewacin kasar. Yace kafin a bude taron an samu takaddama musamman daga 'yan arewa saboda irin dabi'un da aka nunawa yankin inda aka nuna 'yan kudu sun fi arewa yawan wakilai. Sabili da haka ne mutanen arewa suka yi shakku akan tasirin da taron zai yi ga arewa.
Amma zuwa taron ya yiwa arewa alheri. Yayi kyau ga arewa kuma yankin bashi da hujjar komawa baya. Shugabannin arewa da al'ummar yankin sun fahimci cewa zuwan 'yan arewan yana da alfanu. Wakilan arewa sun isa su kare yankin kuma ba matsorata ba ne domin a kowane fanni yankin nada mutane kwararru. Duk abun da wani yake tinkaho dashi arewacin Najeriya tana da abun da ya fi nashi.
A taron an shiga jayayya an kuma kai ruwa rana akan matsaloli amma daga karshenta wakilan arewa sun kare mutuncin arewa. Babu abun asha da za'a ce wakilan sun yi. Dukansu sun taru sun zama da albarka da kuma anfani. Babu abun da taron yayi da ya cutar da arewa.
Dangane da kirkiro sabbin jihohi Sanata Kumo yace an tashi an ce an yiwa arewa alfarma domin ta fi kudu yawan jihohi sai su 'yan arewa suka kare wannan suka musanta zargin. Yayi misali da fafitikar da suka kwashi shekaru ashirin suna yi wurin neman jihar Gombe. Yace kafa jihar ba alfarma aka yi masu ba. Sun nema ne kuma sun cancanta sun kuma cika ka'idodi.
Ga rahoton Sa'adatu Fawu.