Darektar harkokin sadarwa ta Fadar White House Hope Hicks, daya daga cikin amintattun hadiman shugaba Trump tun kafin a zabe shi ta ajiye aiki.
Trump ya fada a wata sanarwa jiya cewa, “Hope tayi fice, ta gudanar da ayyukanta da kyau cikin shekaru uku da suka shige. Tana da basira da hangen nesa, zan yi rashinta matuka. Ta tuntubeni cewa tana so ta maida hankalinta a kan wadansu ayyuka daban, na kuma fahimci haka. Na hakikanta cewa zamu sake yin aiki tare nan gaba”.
Hicks ‘yar shekaru ishirin da tara, wadda ta kasance darektar harkokin sadarwar mafi kuruciya a tarihin Fadar White House, taki amsa tambayoyin da kwamitin tattara bayanan sirri ya yi mata ranar Talata, a zaman da kwamitin ya gudanar a kadaice.
Hicks ta shaidawa kwamitin cewa, wani lokaci akan bukaceta ta danne gaskiya. Sai dai tace bata taba yin karya dangane da abinda ya shafi binciken katsalandan da ake zargin Rasha da aikatawa a zaben shugaban kasa na shekaraR 2016 ba, da dan takar jam’iyyar Republican Trump ya doke abokiyar takararsa ta jam’iyyar Democrat Hillary Clinton.
Facebook Forum