Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dangote Ya Sa Sunan Wigwe A Hanyar Da Ta Shiga Matatar Man Kamfaninsa


Herbert Wigwe
Herbert Wigwe

Aliko Dangote, hamshakin dan kasuwa a Najeriya ya karrama marigayi Herbert Wigwe Shugaban Bankin Access, ta wajen sa sunan marigayin a kan hanyar shiga kamfanin man fetir na kamfanin Dangote.

Dangote ya bayyana Herbert a matsayin amini mai aminci kuma ginshikin mai tallafawa shi da iyalansa, wanda ya zama babin koyi mai kuma hangen nesa da jajircewa da babu irinsa.

“Ina alfaharin kafa sunan abokina, mai bani shawara, mai kuma goyon baya na.” in ji Dangote.

Idan ba a manta ba, Wigwe tare da matarsa da dansa sun mutu ne a wani hatsarin jirgi mai saukar ungulu a ranar 9 ga Fabrairu 2024 a Amurka a kan hanyarsa zuwa gasar Super Bowl LVIII a Las Vegas.

Makonni bayan haka, abokansa da suka hada da hamshakan ‘yan kasuwa na kasar, gwamnoni, da jami’an gwamnati da sauransu sun hallara a cibiyar kasuwanci ta kasar yayin da aka fara bikin binne Wigwe da wani taron mai taken, ‘Celebrating Herbert Wigwe – A Professional Legacy’.

Wasu daga cikin manyan baki da suka halarci taron sun hada da Gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN) Yemi Cardoso; Ministan Kudi da Tattalin Arziki Wale Edun; Shugaban Bankin Raya Afirka Akinwumi Adesina; Gwamna Babajide Sanwo-Olu na Legas; Dapo Abiodun na jihar Ogun da dai sauransu.

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG