Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dandalin Sada Zumunta Na Meta Ya Cire Shafin Mawaki Rarara


Dauda Kahutu Rarara (Facebook/Rarara)
Dauda Kahutu Rarara (Facebook/Rarara)

Rahotannin sun bayyana cewa mabiya Dauda Kahutu Rarara a shafin sada zumunta na Facebook da yawa sun tura sakonnin neman a cire shafin mawakin daga dandalin, saboda wata wakar yabo da ya yi wa gwamnatin Najeriya kwanan nan.

Ga dukkan alama kamfanin sada zumunta na Meta wanda aka fi sani da Facebook ya cire shafin fitaccen mawakin nan dan arewacin Najeriya mai suna Dauda Kahutu Rarara daga dandalin, bayan da mabiyan mawakin suka kai wa kamfanin korafi.

Matakin cire shafin dai na zuwa ne bayan da Rarara ya wallafa wata waka ta yabon shugaban Najeriya Bola Tinubu saboda yadda yake magance matsalolin talauci da tsaro a Najeriya.

A ranar Asabar ne dai aka cire shafin sada zumuntar mawakin na Facebook, wanda ke da mabiya sama da miliyan daya. Wakar da mawakin ya yi ta yaba wa Tinubu kan yadda ya ke kawar da yunwa da rashin tsaro a Arewacin kasar, a cewarsa “yanzu ‘yan Arewa sun yi bankwana da yunwa, rashin tsaro, da talauci.”

Wakar, wadda ta janyo cece-ku-ce dai na zuwa ne a daidai lokacin da ake shirin gudanar da zanga-zangar gama-gari daga ranar daya ga watan Agusta, sakamakon tashin farashin abinci da kuma tabarbarewar tattalin arziki a kasar da ta fi yawan jama’a a nahiyar Afrika.

Duk da yabon da Rarara ya ke wa gwamnatin, a kwanan nan sai da mahaifiyarsa ta yi kwanaki uku a hannun ‘yan bindiga, kafin daga baya suka sako ta.

Dandalin Mu Tattauna

Bidiyo

Saurari Dalilin Da Ya Sa Ummi Zeezee Ta Ce Tana So Ta Kashe Kanta A Hira Da Wakiliyar VOA Baraka Bashir
please wait

No media source currently available

0:00 0:06:39 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

VOA CASU

VOA CASU: Saurari Bayanin Jarumar Kannywood, Nafeesa Abdullahi
please wait

No media source currently available

0:00 0:12:24 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

VOA CASU

VOA CASU: Bikin Yini Na Auren Zawarawa A Kano
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG