Hassan Ayariga da ya kaddamar da jami’iyarsa ta APC kasa da watanni shida da suka wuce, a jawabin da ya gabatar wajen shagalin kaddamar da kundin manufofin jami’iyarsa a birnin Accra, ya yi hasashen cewa shine zai lashe zaben shugaban kasan da za’ayia cikin shekarar nan.
Haka kuma a wata hira da ya yi da Muryar Amurka, Ayariga ya yi Imani yan Ghana zasu ba manufofin nasa goyon baya don kyautata rayuwar al’umma a fadin kasar baki daya.
Kasar Ghana dai tana da manyan jami’iyyu biyu ne, da suka hada da jami’iyar NDC mai mulki da shugaba John Mahama ke jagoranta da kuma babban jami’iyar adawa ta NPP da Nana Addo Dankwa Akufo-Addo ke jagoranta.
Wa’yannan jaimi’iyyu biyu sune ke taka muhimman rawa tun lokacin da Ghana ta koma bisa tarfakin demokaradiya a shekarar 1992 kuma dukkaninsu sun yi nasarori kuma sun sha kaye a zabukan baya.