Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kafa Dokar Ta Baci A Kasar Ethiopia


Dinbin Masu Zanga Zanga Na Maci A Ethiopia
Dinbin Masu Zanga Zanga Na Maci A Ethiopia

Gwamnatin Ethiopia ta kafa dokar ta baci ta tsawon watanni shida, a wani matakin maida martani ga tarukkan zanga zangar kin jinin gwamnati wda aka jima ana gudanarwa a sassan kasar daban-daban.

Pirayim Ministan kasar, Hailemariam Desalegn ya fada a wani jawabinsa na gidan telbijin inda yake cewa wannan dokar da ta fara aiki shekaranjiya Asabar, an kafata ne don a kawo karshen hare haren da ake kaiwa gine ginen gwamnati da wuraren kasuwanci.

Wannan zanga-zangar dai ta samo asalainta ne daga jihar Oromiya a karshen shekarar 2015. Yan zanag zangar da suka fara da neman hakkokinsu na fili, yanzu suna bukatar a kara musu karfin yanci a fannonin siyasa, da tattalin arziki da kuma al’adu.

Kungiyoyin rajin kare hakkin bil adama sun rawaito cewar mutane sama da 450 ne aka kashe a cikin wannan rikicin a wannan shekara.

Ko a ranar Lahadin da ta wuce, mutane 55 ne aka kashe a wani turmustutsu da ya biyo bayan tattaka mutane da aka yi lokacinda ‘yansanda suka saki barkonon tsohuwa don tarwatsa gungun masu zanga zangar a kasar ta Ethiopia.

XS
SM
MD
LG