Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wasu 'Yanbindiga cikin Motoci Ukku Sun Hallaka Sojojin Nijar Kusa da Iyaka da Kasar Mali


 Mahamadou Issoufou SHUGABAN nIJAR
Mahamadou Issoufou SHUGABAN nIJAR

'Yanbindigan da ba'a tantance ba sun kai hari kan sojojin Nijar kusa da kan iyakar kasar da Mali kuma 'yanbindigan sun tsere zuwa cikin kasar Mali din lamarin da ya sa ake kyautata zaton 'yan tawayen kasar ne.

Lamarin ya faru ne a ranar Alhami da misalin karfe biyu na rana inda 'yanbindigan suka shammaci sojojin na Nijar suka kuma kashe ishirin da hudu kana yau wasu hudu suka kara mutuwa daga rauni da suka samu abun da yanzu ya sa adadin sojojin da suka mutu ya kai ishirin da shida.

A garin Tazame ne aka kaiwa sojojin hari dake arewa maso gabashin garin Tasara mai tazarar kilomita arba'in da biyar kuma kilimita tamanin da shiga kasar Mali.

Wani dan jarida dake garin yayi karin bayani. Ya tabbatar duk wadanda aka kashe sojoji ne. Cikin wadanda suka ji ciwo da aka kaisu asibiti hudu sun rasu.

Baicin kashe sojojin ,'yanbindigan sun kone motocin soja da motar daukan masu jinya zuwa asibiti.

Wurin da aka kai harin yana da sansanin 'yan gudun hijira.

Ga rahoton Mamman Barma da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:15 0:00

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG