Babban sifeton 'yansandan kasar ta Kamaru Marchin Barga shi ya jagoranci bude wasu manyan naurori da kasashen turai din suka tanada ma tasoshin.
Naurorin zasu ga irin kayan da fasinjoji ke dauke dasu domin hana 'yan ta'ada shigo da makamai ko bamabamai ko kuma kayan hada bam.
Cikin jawabinsa babban sifeton 'yansandan yace sun yi hakan ne domin su kara inganta tsaro kuma suna shaidawa jama'a masu zirga zirga a tasoshin ana kara kare lafiyarsu ne.
Shi ma shugaban tawagar kungiyar EU Mr. Francois yace zasu kara kawo naurori domin taimakawa 'yansanda domin inganta matakan tsaro a kasashen Afirka musamman wuraren da ake fama da matasalar ta'adanci da kuma masu safaran miyagun kwayoyi.
Malam Suleiman dake aikin zirga zirga a tasoshin jiragen sama yace abun farin ciki ne saboda Kamaru a tsakiyar Afirka kasa ce da ta zama mararraba domin duk abun da ya shiga Kamaru zai kai sauran kasashen kamar su Chadi da dai makamantansu. Naurorin zasu taimaka wurin kama bamabamai ko kayan hadasu.
Ga rahoton Garba Awal da karin bayani.