Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dan Kunar Bakin Wake Ya Hallaka Mutane 22 Da Jikata 59 A Jihar Manchester


'Yan sandan Burtaniya sun ce mutane akalla 22 ne su ka mutu sannan 59 kuma su ka samu raunuka, a fashewar nan da ta auku jiya Litini, a harabar wani wajen rawa a Manchester da ke Ingila.

Hopkins, babban jami'in 'yan sandan Greater Manchester a yau dinnan Talata ya bayyana cewa "Mu na daukar wannan al'amarin a matsayin aikin ta'addanci, kuma a halin yanzu mun yi imanin cewa wani mutum ne ya kai wannan hari na daren jiya,"

Hopkins, ya ce masu bincike sun yi imanin cewa maharin na dauke ne da wani bam hadin gida, wanda ya tayar kuma shi ma ya mutu a wurin.

Firaminista Theresa May, ta ce jami'an 'yansanda da na tsaro sun ce su na kyautata zaton sun san wanda ya kai harin, to amma har yanzu ba su yanke shawarar bayyana sunansa ga jama'a ba.

Daga bisani kuma Rundunar 'Yansanda ta fadi ta kafar Twitter cewa jam'anta sun damke wani mutum dan shekaru 23 da haihuwa a Kudancin Manchester game da wannan harin, amma ba su bayyana alakarsa da harin ba.

Fashewar ta faru ne a farfajiyar dandalin nan na wake-wake da raye-raye na Manchester, wato Manchester Arena, bayan wani shagalin raye-raye da kade-kade na wata ba-Amurkar mawakiya mai suna Ariana Grande.

"Cikin matukar damuwa, kuma daga can cikin zuciyata, na ke cewa ina mai mika jaje na," a cewar Grande a kafarta ta Twitter bayan fashewar, inda ta kara da cewa, "Ban ma san abin cewa ba."

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG