Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wani Sashe Na Rufin Babban Masallacin Zariya Ya Rufta


Daidai inda rufin ginin ya rufta a Masallacin na Zazzau (Hoto: Facebook/Sani Lawal Maqarphy)
Daidai inda rufin ginin ya rufta a Masallacin na Zazzau (Hoto: Facebook/Sani Lawal Maqarphy)

Bayanai sun yi nuni da cewa wasu da dama sun jikkata a ibtila’in wanda ya faru yayin da ake sallar La’asar da misalin karfe hudu na yamma.

Rahotanni daga Zariya a jihar Kadunan Najeriya na cewa mutum hudu sun rasa rayukansu bayan da wani sashe na rufin Babban Masallacin masarautar Zazzau ya rufta a ranar Juma’a.

Bayanai sun yi nuni da cewa wasu da dama sun jikkata a ibtila’in wanda ya faru yayin da ake Sallar La’asar da misalin karfe hudu na yamma, kamar yadda Sarkin Zazzau, Malam Ahmed Nuhu Bamalli ya ce.

Sarki Bamalli a cewar jaridar Daily Trust, ya ce masarautar ta gano wani sashe da ya tsage a rufin ginin Masallacin, kuma ana da niyyar gyarawa kafin wannan al’amari ya faru.

Bamalli ya kuma aika da sakon ta’aziyyarsa ga iyalan wadanda hadarin ya rutsa da su.

Masallacin na Masarautar ta Zazzau, dadadden gini ne mai dumbin tarihi da aka yi ta sauya masa fasali.

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG