A yau laraba Kofin da aka sa a gasar cin kofin duniya da za'ayi a kasar Rasha ya iso Najeriya, hukumar kwallon kafa ta Najeriya, ta bayyana a shafin yanar gizonta a ranar Talata cewa Kofin zai isa filin jirgin sama na Nnamdi Azikiwe, dake Abuja, a cikin jirgin sama da misalin karfe 11 safe.
Kamfanin dillancin labaran Najeriya ya ruwaito cewa kofin zai zaga biranen 91 a kasashe 51 a cikin nahiyoyin 6 kafin gasar cin kofin duniya ta 21.
Ministan Harkokin Matasa da Wasanni, Solomon Dalung, da Sakataren Harkokin Jakadanci Olusade Adesola, da Shugaban hukumar kwallon Kafa ta Najeriya (NFF,) Amaju Pinnick, da kuma wasu za su karbi Kofin daga filin saukar jiragen sama, tare da wasu jami'an, Fifa da suka taho da Kofin,
Daga nan su nufi Transcorp Hilton Hotel don taron manema labaru wadda shugabannin kamfanin Coca-Cola za su daga bisani tawagar Fifa ta isa fadar shugaban kasa inda shugaba Muhammadu Buhari zai yi jawabin maraba.
A ranar Jumma'a tawagar zata bar Abuja zuwa Legas don ganawa da Gwamna Akinwunmi Ambode, Mataimakin Shugaban hukumar na NFF, Seyi Akinwunmi ya karbe su. A ranar Asabar za'ayi gangami a dandalin Tafawa Balewa Square kafin Kofin ya bar Nijeriya da yamma, wannan shi ne karo na uku da kofin ya ziyarci Nijeriya.
Facebook Forum