Hukumar kula da kwallon Kafa ta nahiyar turai UEFA tana tuhumar kungiyoyin kwallon Kafa guda biyu kungiyoyin sune, Paris Saint-Germain, ta faransa da kungiyar Basel, sakamakon abinda magoya bayan su suka aikata a yayin wasannin su na gasar cin kofin zakarun turai na bana.
PSG ana tuhumar na da laifuka guda hudu ciki har da yin amfani da wasan wuta a yayin wasansu na biyu da kungiyar Real Madrid ranar Talata a kasar faransa, inda aka dakatar da wasan na wani lokaci bayan dawowa daga hutun rabin lokaci sakamakon magoya bayan PSG sun kunna wuta kuma hayaki ya cika filin wasan, an dai tashi a wasan Real Madrid ta doke PSG daci 2-1.
Ita ma Basel ana tuhumarta ne da aikata irin wannan hali na kunna wuta a filin wasan su da suka yi da Manchester City a kasar Ingila inda ta doke Man City 2-1 amma duk da haka bata samu nasarar zuwa zagaye na gaba ba sakamakon tuna karawar su ta farko Manchester ta lallasa ta da kwallaye 4-0.
Kwamitin ladaftarwa na Hukumar UEFA zata duba dukkan lamurran karkashin dokokin hukumar ranar 22 ga Maris 2018, domin yanke hukuncin abinda ya dace.
Facebook Forum