Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Za A Yi Nadama Idan Aka Sauke Pantami - Sheikh Gumi


Sheikh Ahmad Gumi
Sheikh Ahmad Gumi

Fitaccen malamin addinin Islama a Najeriya, Sheikh Ahmad Gumi ya ce Najeriya za ta yi da-na-sani, idan har aka cire ministan yada labarai Isa Pantami daga mukaminsa.

‘Yan Najeriya da dama sun yi ta kira a cire Pantami daga mukaminsa na ministan bayan da wasu fayafayen bidiyo da aka dauka a shekarun 2000 suka fito, wadanda suka nuna ministan yana goyon bayan kungiyar Al- Qaeda da Taliban.

Ko da yake, Pantami, ya riga ya ce ya sauya ra’ayinsa kan kungiyoyin ‘yan ta’addan, yana mai cewa matsayar da ya dauka a baya, bisa fahimtarsa ce a lokacin yana matashi.

“Pantami bai mai goyon bayan ‘yan ta’adda ba ne, ku nuna min mutum daya da ya kashe, kuma bai bada umurnin a kashe kowa ba.” Gumi ya fada yayin wata hira da ya yi da Roots TV a ranar Litinin.

“Mutumin (Pantami) yana kawo sauyi a gwamnati, yana janyo hankalin wani rukunin matasa don kwadaitar da su muhimmancin gina ksa, kamata ya yi a ce an samu ire-irensa an saka a gwamnati.” Gumi ya ce.

“Kada ku cire shi, in kuka yi haka, za ku yi da-na-sani.” In ji Sheikh Gumi.

A makon da ya gabata, Ita ma dai fadar shugaban Najeriya ta fito ta mara baya ga ministan, inda ta ce ta kaddamar da wani bincike don gano wadanda suka dauki nauyin kokarin da ake na shafawa ministan kashin kaji.

Isa Pantami
Isa Pantami

Kakakin Shugaba Buhari Malam Garba Shehu, cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Alhamis a Shafin Twitter, ya ce gwamnati ta fara binciken wadanda suke da hannu a yunkurin shafawa ministan kashin kaji.

“A jerin shekarun 2000, ministan yana matashi a shekarunsa na 20, a shekara mai zuwa zai cika 50. Lokaci kan shude, mutane kan sauya matsayarsu.” Garba Shehu ya ce.

Sanarwar tara kara da cewa, abin takaici ne, a ce an dauki wani irin salon tafiya, na dora laifi akan shugabannin siyasa, addini, kungiyoyin fararen hula na yanzu, dangane da wasu kalamai da suka yi a baya, komai dadewar lokacin, ko da ma sun sauya matsayarsu kan abin da suka fada.

XS
SM
MD
LG