Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Najeriya: Fadar Shugaban Kasa Ta Kare Pantami


Isa Ali Pantami (Hoto: Instagram/isaalipantami)
Isa Ali Pantami (Hoto: Instagram/isaalipantami)

Fadar shugaban Najeriya, ta fito ta kare Ministan sadarwa Dr. Isa Pantami da ke fuskantar kiraye-kiraye daga wasu 'yan Najeriya kan ya yi murabus daga mukaminsa.

Kiraye-kirayen sun samo asali ne saboda wasu kalamai da aka daganta da ministan, inda aka ce ya nuna goyon baya ga wasu kungiyoyi masu tattsauran ra’ayi.

Shi dai Pantami tuni ya bayyana cewa ya sauya matsayarsa kan kungiyoyin inda ya bayyana cewa ya janye kalaman nasa, wadanda ya yi su shekaru da dama.

Kakakin Shugaba Buhari Malam Garba Shehu, cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Alhamis a Shafin Twitter, ya ce gwamnati ta fara binciken wadanda suke da hannu a yunkurin shafawa ministan kashin kaji.

“A jerin shekarun 2000, ministan yana matashi a shekarunsa na 20, a shekara mai zuwa zai cika 50. Lokaci kan shude, mutane kan sauya matsayarsu.” Sanarwar ta ce.

Sanarwar tara kara da cewa, abin takaici ne, a ce an dauki wani irin salon tafiya, na dora laifi akan shugabannin siyasa, addini, kungiyoyin fararen hula na yanzu, dangane da wasu kalamai da suka yi a baya, komai dadewar lokacin, ko da ma sun sauya matsayarsu kan abin da suka fada.

“Idan har akwai kamshin gaskiya dangane da labarin cewa an ba wasu editocin gidan jaridu na goro (don su bata sunan Pantami), ya zama dole wadanda suke da hannu, su sa ran ganin gayyatar ‘yan sanda da kotu.”

Garba Shehu ya kara da cewa, "duk dan Najeriya mai hankali ya san cewa, wadannan karerayi da ake yadawa (akan Pantami), ba su da alaka da kalaman da ministan ya yi a baya, sai dai don irin ayyukan da yake yi a yanzu."

A karshen makon da ya gabata, kafofin yada labarai da dama a Najeriya, musamman na yanar gizo, suka wallafa cewa Amurka ta saka Pantami cikin jerin sunayen ‘yan ta’adda, batun da bincike ya nuna ba haka ba ne.

Hakan ya sa ministan ya ce ya zama dole ya dauki matakin gurfanar da su a gaban kuliya.

“Duk manyan kafafen yada labaran da suka bata min suna, za su hadu da lauyoyina a kotu.” Pantami ya ce.

“Laccocina da na kwashe shekara 15 ina sukar masu yada munanan akidoji sunan nan, ciki har da mukabaloli da na yi, wadanda suka saka rayuwata cikin hadari. Idan mutum ba ya jin Hausa, ya nemi tafinta adili mai jin Hausa, ya fassara masa abin da na fada.” Pantami ya fada a shafinsa na Twitter.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG