Bankin na CBN ya yi wannan bayanin ne a wata sanarwa da ya fitar dauke da sa hannun darektan harkokin sadarwa Isa AbdulMumin da aka wallafa a dandalin sada zumunta na bankin X.
Babban bankin ya bayyana cewa, ba shi ya tura sakon ko ta kwana da ake ta tuturawa ba. Bisa ga cewar CBN, wadanda su ka fara yayata wannan sakon, sun saura ainihin abinda tsohon shugaban babban bankin ya tura ne ta sakon a 2oo7.
Bankin ya bayyana damuwa ganin yadda ake ci gaba da yayata wannan sanarwar ta kanzon kurege da ke daukar hankalin ‘yan kasa inda tuni aka fara tafka muhawara a kai duk kuwa da cewa bankin ya karyata wannan batu a lokutan baya.
A shekara ta dubu biyu da ishirin da biyu Bankin CBN ya sauya fasalin takarkun kunin Naira, na N200, N500 da N1000.
Dandalin Mu Tattauna