Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Daliban Ghana Da Ke Sudan Sun Koma Gida


Ghanian parents of Sudan students who came
Ghanian parents of Sudan students who came

Bayan kwashe su daga Sudan a ranar 25 ga watan Afirilun jiya an wuce kasar Habasha da su, daga nan kuma suka hau jirgin saman da ya karaso da su filin jirage na Kotoka da ke Accra a Ghana a ranar Talata 2 ga watan Mayun.

A yayin da ake ci gaba da samun hare-hare ta sama da kasa a birnin Khartoum duk da yarjejeniyar tsagaita bude wuta da aka cimma, wanda bai tafi yadda aka tsara ba.

Ma'aikatar Harkokin Wajen Ghana, a ranar Talata 25 ga watan Afrilu ta yi nasarar jigilar 'yan Ghana daga Jamhuriyar Sudan zuwa kasar Habasha lafiya.

Dalibai 74 suka amince a dawo da su gida Ghana a karkashin kulawar ma'aikatar, kamar yadda karamin ministan kasashen waje, Kwaku Ampratwum-Sarpong da ya wakilci gwamnatin wajen yi wa daliban maraba, ya bayyanawa manema labarai.

Ya kara da cewa, "akwai wasu injiniyoyi biyu da ke aiki tare da wani kamfanin hakar ma'adinai a kan iyakar Sudan da Masar, sun sami damar tsallakawa zuwa Masar tare da taimakon kamfaninsu kuma tuni sun riga sun iso Ghana. Muna da wasu 'yan wasan ƙwallon ƙafa guda huɗu, waɗanda suka tsallaka ta kan iyakar Masar k uma muna shirin dawo da su gida".

Ghaninan parents in a warm embrace with their Sudanese returnee students
Ghaninan parents in a warm embrace with their Sudanese returnee students

Karamin Ministan ya kara da cewa, a halin yanzu babu wani dan Ghana da suka sani cewa yana kasar Sudan, amma duk wanda ya fito da kan sa kuma yana neman taimako, gwamnati a shirye take ta taimaka masa. Domin haka ne ta ba da lambobin wasu jami'anta dake Sudan, Ethiopia da kuma Masar.

parents in a warm embrace with their returning children
parents in a warm embrace with their returning children

Wasu dalibai sun bayyana yanayin wahalar da suka shiga, musamman da yake a mota suka yi doguwar tafiya daga Omdurman zuwa Khartoum zuwa Habasha, sannan kuma suka wuce Adis Ababa, daga nan aka shigar da su jirgin sama zuwa gida.

Su ma iyaye da ‘yan uwan dalibai da suka zo tarbarsu, sun bayyana fargaba da suka shiga da kuma farin cikinsu da yaransu suka iso gida lafiya.

Kasar Sudan dai ta fada cikin kazamin rikici tsakanin dakarun kasar Sudan da dakarun ko ta kwana na RSF, lamarin da ya janyo asarar rayuka da kuma tilastawa kasashe da dama kwashe 'yan kasarsu daga kasar.

A saurari rahoton Hamza Idris:

Daliban Ghana Da Ke Sudan Sun Koma Gida. MP3
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:45 0:00

XS
SM
MD
LG