NARRATION A yayin da al-umomin yankin Birnin Gwari ke kokawa game da hauhawar hare-haren 'Yan-Bindigan da ke hana manoma dibar amfanin gona, gwamnatin Kaduna ta sanar da harbe wasu 'yan-bindiga 6 da kuma kwato makamai da dama a yankunan Birnin Gwari, Giwa da Igabi.
Kaduna, Najeriya —
Cikin mako daya dai 'yan-bindigan sun kai mabanbantan hare-hare a yankunan Birnin Gwari ciki har da Kakangin da su ka bukaci kudi sannan su ka sace mutane.
Malam Ishaq Usman Kasai shine shugaban kungiyar cigaban masarautar Birnin Gwari kuma ya ce hare-haren 'yan-bindigan na damun su. Ya ce ko ranar Laraba ma sai da 'yan-bindigan su ka afkawa garin Kakangi su ka sace mutane goma sannan su ka bukaci a kai mu su miliyoyi.
Tuni dai a ranar Juma'an nan gwamnatin jahar Kaduna ta fidda sanarwar nasara kan 'yan-bindigan da jami'an tsaro su ka kashe shida daga ciki sannan su ka raunata wasu, inji kwamishinan tsaro na jahar Kaduna, Malam Samuel Aruwan.
Ya jadda kokarin da gwamnati ke yi don murkushe 'yan-bindigan dajin da ke yankunan Birnin Gwari, Giwa, Igabi da sauran sassan jahar Kaduna
Shugaban kungiyar cigaban masarautar Birnin Gwari malam Ishaq Usman Kasai ya ce akwai bukatar gwamnatin tarayya ta kai musu dauki.
Dama dai duk farkon damana da karshen ta 'yan-bindiga kan matsawa al-umomin yankunan karkaran da ke noma ta hanyar saka mu su haraji kafin shuka da kuma lokacin girbi.
A saurari rahoton Isah Lawal Ikara:
Dandalin Mu Tattauna