Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wata Kungiya Ta Sayawa Shugaba Buhari Fom Din Tsayawa Takara


Wata kungiya dake goyon bayan shugaba Muhammadu Buhari, ta biyawa shugaban kudin fom din zaben fidda gwani Naira Miliyan 45.

Ita dai wannan kungiya mai taken “Nigeria Consolidation Ambassadors” ta mika takardar fitar da kudi ta banki mai dauke da Naira Miliyan 45 ga shugaban jam’iyyar APC don biyawa shguaba Buhari kudin fom din zaben fidda gwamni.

Shugaban kungiyar, Sunusi Musa, ya ce ba zuba hannun jarin samun riba su ka yi don nan gaba ba, sun yi haka ne don gamsuwar su ga neman tazarcen shugaban.

Haka kuma Sunusi Musa, ya ce hakan ba wai ya nuna don shugaba Buhari ba shi da kudin sayen fom din ba ne amma matakin zai ‘kara ma sa kwarin gwiwa don tsayawa takarar.

A baya dai an yada bayanan da ke nuna shugaban ba shi da kudin fom din tsayawa takarar, domin tun farko kudin fom din Naira Miliyan 55 ne kafin a rage Naira Miliyan 10.

Sakataren jam’iyyar, Mai Mala Buni, ya ce hakan ya nuna irin farin jinin shugaba Buhari da yadda ‘yan Najeriya su ka amince da salon mulkin sa.

Ya zuwa yanzu dai mutum daya ne matashin dan siyasa Adamu Garba, ya baiyana aniyar kalubalantar shugaban a zaben fidda gwani da za a yi ta salon ‘yar tinke.

Domin karin bayani saurari rahotan Nasiru Adamu El-Hikaya.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:56 0:00

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG