A wani taron kolin samar da zaman lafiya a birnin Al-Kahira a yau Asabar, Sakatare-Janar din Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya fadi cewa akwai bukatar motocin agajin su yi hanzarin kai kayayyakin lami lafiya daga Masar zuwa Gaza.
Ya kuma godewa Masar saboda rawar da ta taka wajen taimakawa kai agajin.
"Amma al'ummar Gaza na bukatar a ci gaba da kai karin agajin, iya adadin da ake bukata," a cewarsa. Ya kara da cewa, "Muna aiki ba dare ba rana da duk bangarorin da suka dace don ganin hakan ya faru."
Jerin manyan motoci sun kwashe kwanaki da dama a kusa da mashigar Rafah suna jira a bude iyakar don kai agaji ga mazauna Gaza su fiye da miliyan biyu.
A cikin wata sanarwa shugaban hukumar kula da ayyukan jinkai na Majalisar Dinkin Duniya Martin Griffiths, ya tabbatar da cewa kungiyar agaji ta Red Crescent ta Masar da Majalisar Dinkin Duniya sun samar da motocin kayayyakin jinkai da ake matukar bukata. Ya ce an amince su tsallaka zuwa Gaza kuma kungiyar agajin Red Crescent ta Falasdinu za ta tarbe su, tare da taimakon Majalisar Dinkin Duniya.
Ayarin motocin shi ne na farko da aka ba izinin shiga Gaza ranar Asabar tun bayan da kungiyar Hamas ta kaddamar da harin ba-zata a kan Isra'ila a ranar 7 ga watan Oktoba, wanda ya yi sanadin mutuwar mutane kimanin 1,400, lamarin da ya sa Isra’ila kai farmaki da kuma yi wa Gaza kawanya. Falasdinawa sama da 4,000 aka kashe.
Dandalin Mu Tattauna