Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Da Gaske Gwamnoni Suka Ruguza Yunkurin Sanatoci Kan Zartar Da Gyaran Dokar Zabe?


Taron Yan Majalisa Da Sanatoci Da Aka Yi A Hade
please wait

No media source currently available

0:00 0:00:05 0:00

Taron yan majalisa da sanatoci da aka yi a hade.

Rahotanni sun yi nuni da cewa yunkurin da wasu 'yan majalisar dattawan Najeriya suka yi na yin watsi da matakin shugaban kasa Muhammadu Buhari game da kudirin gyaran dokar zabe ya hadu da cikas ne sakamakon matsin lamba daga gwamnonin jihohinsu.

Biyo bayan wasikar da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya aikewa majalisar dattawa, inda ya bayyana kudurinsa na kin amincewa da daftarin gyara ga dokar zabe, ‘yan majalisar sun gabatar da kudirin yin watsi da matakin nasa kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Sai dai matakin na su ya hadu da cikas, a yayin da gwamnoni da sauran masu ruwa da tsaki na jam’iyyar APC mai mulki suka yi tattaki zuwa Abuja a daren ranar Talata, inda suka gana don cimma matsaya kan lamarin, inda kuma suka karyata adadin ‘yan majalisar dattawan da rahotanni suka ce sun rattaba hannu kan yin watsi da ikon matakin na Buhari.

Majalisar dattawa da ta wakilai dai za su bukaci goyon bayan kashi biyu bisa uku na kuri’un da aka kada domin yin watsi da matakin na Buhari ne don zartar da gyaran kudirin zuwa doka.

Kazalika, rahotanni sun nuna cewa ‘yan majalisar ba za su iya cimma hakan ba, saboda jajircewar da wasu masu iko suka yi, lamarin da ya sa wasu sanatoci ke kan sauya salon aikinsu.

Wata majiya ta ce gwamnoni suna da tasiri sosai idan ana maganar yanke shawara a matakin jiha da kasa baki daya.

Haka kuma, wata majiya mai tushe ta ce gwamnonin jam’iyyar APC da dama da wasu daga jam’iyyar adawa ta PDP sun kira sanatocin inda suka bukaci su yi watsi da duk wani yunkuri na sha gaban karfin ikon matakin shugaba Buhari kan gyaran dokar zaben.

Shugaba Buhari a wata wasika da ya aikewa majalisar dokokin kasar mai dauke da kwanan watan 13 ga Disamban shekarar 2021 mai taken ‘Kin amincewa da dokar zabe ta shekarar 2021’ ya ki amincewa da kudirin, bisa dalilan da suka shafi tattalin arziki, tsaro da bangaren shari’a.

A yayin da shugaba Buhari ke ganin rashin dacewar batun soke sasanci a zabukan fitar da gwani kamar yadda sashe na 87 na dokar zabe ta shekarar 2010 ya tanadar, Buharin ya ce gyaran da aka gabatar ya saba wa tsarin mulkin dimokuradiyya, wanda ke da ‘yancin yin zabe.

A cewar shugaban, gyaran zai kuma dakushe kananan jam’iyyu ba tare da ba su dimbin albarkatun da ake bukata don tara dukkan mambobinsu a zaben fidda gwani ba, ya na mai cewa hakan ba tsari ne mai inganci ko dorewar yawan jam’iyyu da dimokradiyya a Najeriya ba.

A zaman majalisar da aka yi a ranar Talata, sanatoci da dama sun ce dalilan da shugaban kasa ya gabatar ba su da kwari kuma sun yi yunkurin tattara sa hannun mambobin majalisar dattawan na yin watsi da ikon shugaban kasar, kamar yadda sashe na 58 sakin sashi na 5 na kundin tsarin mulkin kasar na 1999 da ya tanada.

Sashi na 58 sakin sashi na 5 na kunden tsarin mulkin kasar na shekarar 1999 ya ce ce, idan shugaban kasa ya ki amincewa da wani kuduri, su kuma majalisun dokokin biyu suka jefa kuri’un amincewa da kudurin da kashi biyu bisa uku, kudurin zai zama doka kuma ba za'a bukaci amincewar shugaban kasa ba.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG