Ministar ayukkan jin-kai tare da ta lamurran mata ne suka jagoranci soma bayar da tallafin a Sakkwato.
Kayan tallafin da mutanen suka soma karba sun hada da nau'o'in abinci daban-daban, kayan gini da kayan amfanin cikin gida domin taimaka ga halin kunci da suka shiga sanadiyar ambaliyar da aka fara samu a Sakkwato tun cikin watan Agusta wadda ta yi sanadiyar hasarar rayuka da dukiyoyin na miliyoyin nairori.
Bisa ga yawan hasarar da aka samu ko yaya wannan tallafin zai yi tasiri ga wadanda suka same sa.
Bayan tallafin rage radadin musibar ambaliya haka ma ministar ayukkan agaji da tallafin rage musibu Sadiya Umar Faruq ta jagoranci kaddamar da wani shiri na gwamnatin tarayya na rage fatara ga matan karkara, inda za'a baiwa kowace mace naira dubu 20 domin bunkasa tattalin arzikinsu, inda mata sama da 150,000 za su samu tallafi a jihohi 36 da Abuja.
Ministar lamurran mata Dame Paulen Tallin ta shawarci ne akan wasu matsaloli na daban wadanda ke tarnaki ga ci gaban kasa da kuma walealar al'umma.
To sai dai sau da yawa irin wannan tallafin akan kaddamar da bayar da wurin bukukuwa amma daga baya kuma a samu ko sauya akalar rabon kayan tallafin ko kuma daukar dogon lokaci kafin a ci gaba da shi tamkar yadda ya faru a rabon tallafin kayan rage radadin da cutar korona ga musakai a karamar hukumar Sokoto ta arewa.
Facebook Forum