Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dole a Tura Dakaru Zuwa Burundi - Ban


Sakataren Majalisar Dinkin Duniya, Ban Ki-moon, ya yi kira ga shugabannin kasashen Afirka, inda ya ce bai kamata a rinka nuna jinkiri ba wajen kokarin shawo kan rikicin kasar Burundi domin mutane na ci gaba da mutuwa.

Yayin da ya ke ganawa da manema labarai a gefen taron kolin kungiyar kasashen Afrika da ke gudana a Habasha, Mr. Ban ya kwatanta rikicin na Burundi a matsayin wani lamari da ya kamata a tashi a kare mutuncin dan adam.

Ban ya kara da cewa hakki ne da ya rataya a wuyan shugabannin kasashen Afrika su yi magana da muryar daya, ya kuma yi kira ga shi kansa shugaba Pierre Nkurunziza, da ya samar da damar da za a zauna a teburin tattaunawa da dukkanin bangarorin da ke takaddama a kasar.

A wani jawabi da ya yi a gaban taron a jiya Asabar, Ban ya ce tura dakarun wanzar da zaman lafiya ya zama dole, sai dai gwamnatin kasar ta ce yin hakan tamkar mamaya ce ta yaki.

Kungiyar tarayyar kasashen Afrika na duba yuwuwar tura dakaru 5,000 domin dakile rikicin da ya barke a bara, bayan da shugaba Nkurunziza ya ayyana shirinsa na neman wa’adi na uku, lamarin da ‘yan adawa suka ce ya sabawa kundin tsarin mulkin kasar.

Tuni dai shugaban ya lashe zaben da aka yi a baran.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG