Kawo yanzu kimanin mutane ashirin ne suka mutu sakamakon kamuwa da cutar zawo da amai ko kwalara a jihar Neja. Bayyanai sun nuna sama da mutane arba'in ne suka kamu da cutar a wasu kauyuka biyu dake karamar hukumar Mashegu.
Mai unguwar kauyen Gada, Malam Haruna Zaure, daya daga cikin kauyukan da cutar ta bulla ya sallake rijiya da baya sakamakon kamuwa da yayi da cutar. A kauyen kawai mutum takwas suka rasu kana wasu ashirin suna kwance.
Umar Jibril Igede mataimakin shugaban karamar hukumar Mashegu yace a iyakar saninsu mutane 17 suka tabbatar da mutuwarsu.Ya nemi doki daga gwamnatin jihar Neja domin a dakile yaduwar cutar.
Gwamnatin jihar tace tana da masaniyar bullar cutar kuma tuni ta tura jami'anta na kiwon lafiya yankin domin kai doki tare da binciko dalilin bullar cutar. Hajiya Hadiza Abdullahi kwamishaniyar ma'aikatar kiwon lafiya tace suna da labarin al'amarin kuma sun tura ma'aikata.
Ga rahoton Mustapha Nasiru Batsari.