Shugabannin Nigeria, Kamaru, Nijer, Chad da Benin sun halarci taro a Paris kan Boko Haram.
Shugabannin kasashen Afrika biyar da suka hada da Nigeria, Nijer, Kamaru, Chad da Benin sun halarci wani taron koli da shugaban Faransa Francois Hollande ya gayyata don a tattauna yadda za’a tinkari kalubalen da kungiyar ‘yan tsageran Boko Haram ke tayarwa a kasashen Afrika ta Yamma da ta Tsakiya, musamman a Nigeria. Daya daga cikin manyan batutuwan daaka tabo a taron shine yadda za’a samu hanyoyin ceto ‘yan matan nan sama da 200 ‘yan makaranta na Nigeria da kungiyar Boko Haram din tayi gaba da su a jihar Borno. Kan wannan taron ne, Aliyu Mustaphan Sokoto ya zanta da Seiddik Abba Mamadou, babban editan mujallar “Jeune Afrique” dake can Paris: