Bam din da ya fashe yayi sanadiyar mutuwar mutane biyar har da wanda ya tuka motar dake dauke da bam din.Wasu da dama kuma sun jikata lokacin da bam din ya tarwatse da misalin karfe goma da rabi na dare. Hakazalika kimanin motoci shida dake wurin da lamarin ya faru sun kone kurmus.
Wurin da bam din ya tarwatse wuri ne inda jama'a ke shakatawa. Bam din ya fashe ne a tsakiyar titi abun da ya sa ana zaton mai kunar bakin waken bai kai inda ya nufa ba kafin bam din ya tashi.
Jim kadan da fashewar bam din kwamishanan 'yan sandan jihar Kano ya bayyana a wurin tare da wasu jami'ansa da suka hada da kakakin 'yan sandan Kano ASP Magaji Musa Majiya. Shi kakakin yace suna son su san wace iri ce motar da kuma lambarta. Yace cikin wadanda suka mutu akwai 'yar yarinya mai shekaru goma sha biyu ko sha biyar. 'Yan sandan kula da bama sun isa wurin kuma tuni suka gama nasu aikin. Sauran jami'an tsaro sun share wurin domin su tabbatar babu wani bam kuma a wurin.
Kusan shekara guda ke nan da Kano taba fada cikin wani harin bama-bamai ba abun da ya inganta farfadowar harkokin kasuwanci da na yau da kullum.
Ga rahoton Mahmud Ibrahim Kwari.