Sakatariyar harkokin wajern Amurka Hillary Clinton ta fara ziyara aiki a Burma da zai shiga tarihi, da wan nan ziyara Madam Clinton ta kasance babbar jami’ar difilomasiyyar Amurka, da zata ziyarci kasar cikin shekaru hamsin.
Yau laraba ta isa fadar kasar Naypyitaw dake can da nesa.A ziyarar na kwana uku zata gana da shugaban kasar Thein Sein da kuma shugabar rajin demokuradiyya Aung San Suu kyi.
Sakatariya Clinton wacce ta tashi zuwa Burma daga KTK ta gayawa manema labarai cewa zata tantancewa kanta niyyar gwamnatin kasar Burma na ci gaba da aiwatar da sauye sauye ta fuskar tattalin arziki d a kuma siyasa.
Tayi magana kan abinda shugaban Amurka Barack Obama ya fada a farkon watan nan na alamun ci gaba da aka afara gani na kwariya kwariyar gwamnatin farar hula akasar da ta fara aiki a farkon shekaran nan, bayan fiyeda shekaru 40 na mulkin soja.