Rahoton da Kungiyar lafiya ta duniya ya bayar ya yi nuni da cewa, wannan cuta mai yawan yaduwa itace kan gaba a wajen mutuwar kananan yara a duniya gaba daya, musamman talakawa, marasa abinci mai kayan gina jiki da kuma marasa rigakafi.
An sami nasarar shawo kan bakon dauro a kasashen arewaci da kudancin Amurka, yayinda kuma yammacin sashin Pacific suna kan hanyar kawar da shi, amma yammacin Turai na baya wajen haka domin rashin allurar rigakafi, bisa ga bayanin majalisar dinkin duniya.
Rahoton ya nuna cewa, an sami karuwara yaduwar wannan cutar a kasashe da dama da suka hada Demokaradiyar Congo, India da Nigeria.