A jiya Talata, Cibiyar Hudaibiyya ta nazari da raya harkokin addinin Islama, wadda ke da shalkwata a Kano, ta gudanar da taron lacca kan shugabanci da makomar al'umma, a wani bangare na bibiyar cigaba da kuma kalubalen Najeriya cikin shekaru 59 da samun 'yancin kai.
Dan Masanin Dutse, Alhaji Adamu Aliyu Kiyawa na daya daga cikin wadanda su ka yi tanbihi a wurin laccar wadda ta gudana a kwalejin nazarin shari’ar Musulinci ta Aminu Kano.
Malamai da daliban jami’a da sauran makarantun ilimi mai zurfi, kana da dinbin al’ummar gari ne suka halarci gangamin laccar.
Dr. Hakeem Baba-Ahmed na daga cikin wadanda suka gabatar da Makala a zauren taron, kuma ya yi Karin haske dangane da kunshin makalar tasa, inda ya jaddada muhimmancin shugabanci na gari wanda ke tasiri kan makomar al'umma.
Tsohon gwamnan Kano Sanata Ibrahim Shekarau, wanda yana cikin magabatan cibiyar ta Hudaibiyya, ya yi tsokaci game da cikar Najeriya shekaru 59 da samun ‘yanci.
Dinbin matasa da suka halarci gangamin laccar daga ciki da wajen jihar Kano sun tofa albarkacin bakinsu, inda su ka yi ta cizawa su na hurawa.
Tsohon shugaban hukumar zabe ta Najeriya Farfesa Attahiru Jega da shugabar Jami’ar Tarayya dake Dutse a jihar Jigawa, Farfesa Fatima Batulu Mukhtar, sun gabatar da jawabai daban daban.
Ga cikakken rahotan wakilin Muryar Amurka daga kano, Mahmud Ibrahim Kwari.
Facebook Forum