A daidai lokacin da Najeriya ta cika shekaru 59 da samun ‘yancin kai daga turawan mulkin mallaka, ana ci gaba da gudanar da bukuwa a fadin kasar.
Gwamnatin tarayya da ta jihohi sun gudanar da bukukuwan tunawa da wannan rana, inda suka gabatar da jawabai akan nasararo da ire-iren kalubalen da Najeriya ke fuskanta, dangane da kawo ci gaba da kuma walwala ga al’ummar kasa baki daya.
Bukin na yau Talata ya gudana ne da wani bayani na musamman da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yi tun da safe, inda ya tabo fannoni daban-daban tun lokacin da aka zabe shi a matsayin shugaban kasa a shekarar 2015.
Shugaban Buhari, ya tabo wasu dalilai da suka sa aka zabe shi, da suka hada da yaki da cin hanci da rashawa da samar da tsaro da bunkasa tattalin arziki da kawo walwala akan sha’anin noma ga ‘yan ‘kasa, dama duk wasu abubuwa da ya yi alkawari a lokacin yakin neman zabensa. Ya ce yanzu haka idan ‘yan Najeriya suka auna da ayyukan da gwamnatocin baya suka yi, to zasu ga sauyi.
Haka kuma shugaba Buhari ya yi amfani da jawabinsa wajen nuna nasarorin da aka samu na farfadowa da tattalin arziki da kuma yaki da ta’addanci musamman yakin da ake yi da kungiyar Boko Haram.
Domin Karin bayani saurari rahotan Umar Faruk Musa.
Facebook Forum