Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

China Ta Gargadi Yan Kasarta Dake Kasar Pakistan


China ta gargadi ‘yan kasarta dake zaune da Pakistan da su bi a hankali, tana mai cewa ta sami wasu bayanan sirri dake nuna cewa ana shirin kai wani harin ta’addanci a Pakistan.

Ofishin jakadancin China dake birnin Islamabad ya kafe wani gargadi da ba a saba gani ba a shafinsa na yanar gizo, yayin da Beijing ta saka hannun jari na sama da dala biliyan 60 a Pakistan.

A cewar sanarwar da Ofishin Jakadancin China ya fitar, na cewa “An fahimci cewa ‘yan ta’adda na shirin kai hare-hare kan kamfanonin China da jami’ansu a Pakistan.

Sai dai sanarwar bata bayar da wani cikakken bayani kan irin baranar ‘yan ta’addar ba, amma ta yi kira ga dukkan ‘yan asalin China da su inganta sha’anin tsaronsu, su tsagaita tafiye-tafiye da kuma gujewa duk inda mutane ke taruwa da yawa.

Sanarwar ta nemi ‘yan kasar da su baiwa jami’an tsaro na ‘yan sanda da sojojin Pakistan hadin kai, su kuma sanar da ofishin jakadanci idan suna bukatar agajin gaggawa. Ya zuwa yanzu dai jami’an tsaron Pakistan basu yi wani bayani ba kan gargadin da China ta yi.

Jami’ai dai sunyi kiyasin cewa akwai ‘yan kasar China kusan 20,000 da yanzu haka ke zaune a Pakistan, inda China da kamfanoninta ke gudanar da wasu ayyuka har kusan 300 a kasar.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG