Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Matasa Kiristoci Sun Ba Sufeto Janar Na 'Yan Sanda Wa'adin Makonni Biyu Ya Rufe Sakateriyar Kungiyar Ko Su Mamaye Ta


Reshen matasa na kungiyar kiristocin Najeriya CAN, bangaren jahohin arewa sun ce an tafka magudi a zaben da aka gudanar na shugaban kungiyar, lamarin da suka ce baza su taba yarda da shi ba.

Mr Ezra Yaro, da ke zaman shugaban matasan kiristocin jahar Nasarawa shine yayi Magana da yawun matasan kamar haka, “an yi mana rashin mutumci, kuma an nuna mana cewa yanzu ba maganar addini ake yi ba, domin kuwa wannan zaben mu ‘yan arewa bamu amince da shi ba”.

Ya kara da cewa “babban dalilin cewa hakan shine, mun je da dukkan wakilan mu kuma mun tabbatar dan arewa ne zai lashe zaben amma sai kaga mutum mai suna Emeka kuma ya ce maka wai shi ke wakiltar jihar Gombe! Ta yaya haka zata yiwu?.”

Matashin ya bayyana cewar an yi amfani da kudi ne kawai wajan yin magudin zaben, dan haka a cewar sa, sun ba sufeto Janar Na ‘yan sandan Najeriya wa’adin makonni biyu ya rufe sakateriyar kungiyar kokuma su mamaye ta, domin a cewarsu lallai ba’a yi masu adalci ba.

Saurari rahoton hasan maina kaina.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:18 0:00
Shiga Kai Tsaye

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

XS
SM
MD
LG