A Najeriya rahotanni sun bayyana cewa an sace wasu ma’aikatan kasashen waje misalin su bakwai a garin Clabar dake jihar Cross Rivers a yankin Niger Delta, rahotannin sun bayyana cewa uku daga cikin wadanda aka sace ‘yan asalin kasar Australia ne, biyu daga ciki kuma ‘yan Najeriya da kuma ‘yan kasar Afirka ta Kudu.
Rahotannin sun bayyana cewa ‘yan bindigar matasa ne masu yawan gaske, kuma sun yiwa motar da ma’aikatan ke ciki kwanton bauna a lokacin da suke tafiya cikin garin na Calabar, inda suka hallaka direban motar sa’annan suka yi awon gaba da ma’aikatan kamfanin.
Rundunar ‘yan sandan jihar sun bada tabbacin aukuwar lamarin kamar yadda kwamishinan ‘yan sandan jihar Mr Jimo Ozi ya shaidawa manema labarai inda yace suna kan gudanar da wani aiki na hadin gwiwa tare da sojojin ruwa domin ganin cewa sun ceto wadanda aka yi garkuwa dasu.
Ibrahim Baba, AIG kuma mai fashin baki wanda ya taba yin aiki a jahar ya bayyana cewa hanya guda daya ce ta shiga da fita cikin Calabar, dan haka tunda wadannan mutane suka gano cewa suna iya aikata ta’asa sa’annan su fada cikin jirgin ruwa su gudu, lallai akwai aiki gaban ‘yan sanda da sojoji.
Ya kara da cewa in baya ga yanzu, da wuya a sami gari mai kwanciyar hanali kamar Calabar, dan haka dole ne gwamnati ta tashi haikan wajan ganin ta kare wadannan ma’aikata da kuma sauran ma’aikatan da ke gudanar da ayyuka a wuraren.
Saurari cikakken rahoton a nan.