Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Fursunoni Sun Arce Daga Gidan Kaso Na Koutoukale A Jamhuriyar Nijar


Shugaban Nijar, General Abdourahmane Tiani,
Shugaban Nijar, General Abdourahmane Tiani,

Ma’aikatar cikin gida ta jamhuriyar Nijar tace ta bada umurni ga bangarorin jami’an tsaro dabam dabam domin kasancewa cikin shirin ko ta kwana, bayan da fursunoni su ka arce daga gidan kaso mai tsaron gaske na Koutoukale, da fursunonin da ke ciki suka hada da mayakan kungiyar jihadin Musulunci.

To sai dai sanarwar ma’aikatar ba ta fadi adadin fursunonin da suka tsere daga gidan kurkukun na Koutoukale ba, wanda ke a nisan kilomita 50 daga arewa maso yammacin babban birnin kasar Yamai, ko kuma yadda aka yi su ka tsare ba. An dai rika dakile yunkurin arcewa daga gidan wakafin da fursunoni suka rika yi a shekarun 2016 da 2019.

Fursunonin da ke tsare a gidan kurkukun sun hada da wadanda aka tsare daga rikicin kasashen Afrika ta yamma na kungiyoyin da ke da alaka d al Qaeda da kungiyar kafa kasar musulunci ta IS da mayakan Boko Haram.

Hukumomi a kasar sun sanya dokar hana fita a cikin dare, a yankin birnin Tillaberi da gidan kurkukun yake, ba tare da ba da wani karin bayani ba. Nijar da makwabtan ta da ke yankin tsakiyar yankin Sahel na fama da tatagurza da barazanar kungiyoyin masu fafutukar jihadi, da ya rika ruruwa sannu a hankali tun shekarar 2012, lokacin da mayakan da ke da alaka da al Qaida su ka kwace wasu sassan kasar Mali.

An kashe dubban mutane a tashe tashen hankullan, kuma sama da mutane miliyan uku su ka daidai ce, lamarin da ya zurfafa matsalar ayyukan jinkai a wasu matalautan kasashe na duniya.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG