Masu gabatar da jawabai da mambobin kwamitin a taron zasu kunshi manyan jami’an farar hula da na soja, a cewar Laftanar Kanal Bobby Dixon, mai magana da yawun rundunar sojin Amurka a Afirka da ake kira AFRICOM.
Dixon ya ce, "Manufar taron ita ce tunkarar kalubalen tsaro a nahiyar Afirka da kuma gano hanyoyin aiki tare don samar da tsaro da kariya a Afirka. Kama daga kokarin yaki da ta'addanci zuwa barazanar kutsen yanar gizo da ayyukan wanzar da zaman lafiya, taron zai tattauna a kansu duka.
Rundunar AFRICOM ta ce taron zai dora kan nasarorin da aka samu a tarukan baya. Taron da aka yi a shekarar da ta wuce a birnin Rome na kasar Italiya, ya samu mahalarta mafi yawa, inda kasashe 43 suka tattaru.
Bayan taron kili kan harkokin tsaro da aka yi a watan Maris, Kungiyar Tarayyar Afrika ta bayyana matukar damuwa kan karin tashin hankali da ake fuskanta a nahiyar da kuma tasirin shi ga ci gaban nahiyar da zamantakewar al'umma.
Dandalin Mu Tattauna